<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 1) Ya ku ƴanuwa, bar bin duniya,
 Ta da murya domin Yesu.
 Yafa makamai, dukansu sosai,
 Shiga Yaƙin Ubangijinmu.

[V2]
 KORUS
 Tashi zuwa yaƙin Almasihu,
 Tuƃe nauyin kayan duniya,
 Gaba dai, ba za mu waiwaya ba,
 Ubangiji Shugabanmu ne.

[V3]
 2)  Kome jaraba, muna cin gaba,
 Lalle za mu ci nasara.
 Ikon magauci ba mu raina ba,
 Amma dai ba za mu bi shi ba.
 Korus

[V4]
 3) Ubangijinmu, ji addu'armu,
 Ba bayinka dai ikonka.
 Muna dogara ga Maganarka,
 Mu da kanmu ba mu iya ba.
 Korus

[V5]
 4) In mun gama nan, za mu huta can
 Gidan Allahnmu har abada.
 Ladan aikinmu yana jiranmu,
 In mun yi shi da aminci fa.
 Korus</lyrics>
<title>Ya Ku Ƴanuwa, Bar Bin Duniya LW287</title>
<hymn_number>287</hymn_number>
</song>